Wani matashi mai suna Umar Yusuf dan shekara 22 na fuskantar shari’a a kotun majistare dake garin Sokoto bayan an kama shi da laifin danne wani yaro dan shekara 10 a dakin sa.
Wanda ya shigar da karar Saminu Buke ya bayyana wa kotu cewa Umar ya aikata wannan lalata ne a unguwar Marna, dake garin Sokoto.
Ko da yake Umar ya musanta wannan zargi da ake masa, duk da haka kotu ta ce a ci gaba da daure shi a kurkuku sai ranar 6 ga watan Afrilu da za a ci gaba da shari’ar.