An fara sakin sakamakon jarabawar JAMB

0

Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i na Kasa JAMB ta fara sakin sakamakon jarabawar da aka rubuta a makon da ya gabata.

Kakakin hukumar Fabian Benjamin ya sanar da haka wa PREMIUM TIMES ranar Talata inda ya kara da cewa sai da suka tattance sakamakon jarabawar sannan suka saki.

” Za mu saki sakamakon jarabawar ne kadan kadan har zuwa lokacin da za a kammala.”

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa hukumar ta ce baza ta saki sakamakon jarabawar ba sai ta tattance kuma ta tabbatar cewa babu inda aka algusshu ko satan ansa.

Benjamin ya ce wadanda suka rubuta jarabawar a cikin makon da ya gabata za su iya duba sakamakon su ta yanar gizo a shafin hukumar.

A karshe wani Segun Abidoye wanda ya rubuta jarabawar ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa shi har ya ga nashi sakamakon jarabawa.

Za a kammala rubuta jarabawar JAMB din ne ranar 17 ga watan Maris.

Share.

game da Author