An babbake wani barawon waya a Nasarawa

0

A ranar Litinin din makon nan ne wani barawon waya ya gamu da fushin matasa inda bayan an kama shi ya na kokarin sace wayar wata mata mai dauke da tsohon ciki sun lakada masa dukan tsiya sannan suka babbake shi.

Wannan abu dai ya faru ne a garin Mararaba Gurku jihar Nasarawa.

Wani da abin ya faru a gaban sa mai suna Martins Ago ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa shi dai wannan barawo ya fizge jakar matan ne a daidai ta fito bankin.

” Barawon ya nemi ya fizge jakar matar ne ita ko ta rike jakar tamau, da ya ga abin ya gagara sai ya hambareta a ciki, ba a yi wata-wata ba matar ta fadi kasa tana ihu, Kafin kace tak ko mutane suka yi ram da shi suka dunga jibgar sa. Daga nan aka saka masa taya suka babbake shi.

Sanadiyyar naushi da yayi wa matar ta rasu bayan dan wani lokaci.

Ago yace kafin su kona barawon sun caje aljihun sa inda suka tsinto guduma da kusoshi wanda sanin kowa ne cewa a kwanakin bayan wasu mutane sun yi ta kashe ‘yan achaba ta hanyar buga musu kusa a kansu Idan za su kwace baruran su.

Share.

game da Author