Akwai kwararan alamomin rikici tsakanin Majalisar Tarayya da wasu Ministoci biyu na Ma’adinai da Karafa, yayin da suka nuna rashin samun damar halartar zaman mahawara a majalisa a yau Alhamis.
Dama dai an dade ana ci gaba da kafsa mahawara daban-daban, amma ta ranar Alhamis an bayyana cewa za a yi ne a bangaren harkokin karafa, musamman ta yadda za a farfafo da kamfanin sarrafa karafa na Ajaokuta da ke jihar Kogi.
Yayin da mambobin majalisa ke tunanin farfado da masana’antar ta Ajaokuta, su kuma ministocin sun karkata ne wajen shawarar a sayar da kamfanin ga ‘yan kasuwa kawai.
PREMIUM TIMES ta kawo rahoton inda Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara ya ce tilas gwamnatin tarayya ta yi duk wani kokarin da za ta iya yi domin ta farfado da masana’antar sarrafa karafa ta Ajoakuta, kai ko da kudade za ta ramto, to ta ramto a farfado da kamfanin.
Tun cikin makonni da suka wuce ne majalisar ta gayyaci Ministan Ma’adinai, Kayode Fayemi, Karamin Ministan Ma’adinai, Bawa Bwari da Ministar Harkokin Kudi, Kemi Adeosun da ma wasu da dama, su je a yi mahawara.
To a yanzu PREMIUM TIMES ta samu labarin Ma’aikatar Kula Albarkatun Kasa ta aike wa majalisa wasika cewa ministocin biyu ba za su samu damar zuwa zauren majalisa domin a tafka muhawarar da su ba.
Sun bayar da dalilan cewa dukkan su su na da ayyukan da ke gaban su wanda ya jibinci gudanar da mulkin su.
Sai dai kuma hakan bai yi wa Kakakin Majalisa dadi ba, inda ya maida amsar wasikar a rubuce, wadda Shugaban Ma’aikatan sa, Jerry Manwe ya saw a hannu tun jiya Laraba, cewa idan ma gaba dayan su ba za su iya zuwa ba, to kamata ya yi ko da daya daga cikin su ne ya halarta, saboda muhimmancin batun da za tattauna din.
Dogara ya ce majalisa ba za lamunci irin kulli-kurciyar da ake yi da wasu ministoci ba idan wani batu mai muhimmanci ya taso kuma ana neman su a majalisa.
PREMIUM TIMES ta tuntubi kakakin yada labaran Minista Kayode Fayemi, ya ce bai san da wasikar gayyatar ministan zuwa majalisa ba.