Abin da APC za ta gaggauta yi kafin zaben 2019 -Shehu Sani

0

Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Shehu Sanai ya bayyana cewa tilas sai APC ta gaggauta sasanta rigingimun da ke cikin jam’iyyar kafin zaben 2019, idan ta na so ta tsira da mutuncin ta sannan ta yi haihuwar da mai ido.

Sani ya yi wannan kalami ne a wurin wani taro da aka shirya a ofishin Kungiyar ‘Yan Jaridu ta Jihar Oyo, da ke Ibadan.

Sani shi ne Shugaban Kwamitin Kula da basussukan cikin gida da na kasashen waje.

Ya ci gaba da cewa tun a cikin 2015 bayan an yi nasara sai jama’iyyar APC ta rifta cikin rikice-rikice, wadanda sai fa an shawo kan su tukunna kafin a yi nasara a zaben 2019.

Ya kara da cewa ya yarda da yadda kwamitin Sanata Bola Tinubu ya fara aikin sasanci da kafar dama, don haka ya na da yakinin zai yi nasara.

Ya ce daga cikin rigingimun da ya kamata a shawo kai akwai ta tsakanin sanatoci da gwamnoni da kuma uwar jam’iyya da mambobin majalisar Tarayya.

Ya kuma yi nuni da sabani tsakanin majalisa da ministoci da kuma ita kanta gwamnatin.

Da ya ke tsokaci kan wasu rigingimu da yake ta lashe wasu jihohin, Sani ya ce saboda rashin jituwa a wata jiha, har rusa ofishin jam’iyya gwamnan jihar yayi. Ka ga haka idan da za a amince da kafa ‘yan sandan jiha da Allah kadai ya san abin da zai faru.

Ya ce Jam’iyyar na cikin hayaniya matuka da ssai an gaggauta kawo karshen haka ko ta kuka da kanta.

Share.

game da Author