Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya Moshood Jimoh ya nuna wa manema labarai wasu matasa biyu da ake farautar su da manyan bindigogi a garin Lokoja.
Matasan dai ana zargin suna wata Kungiyar ‘yan ta’adda ne da ake zargin Sanata Dino ne ke yi wa Kungiyar hidima sannan shine ya siya musu bindigogi domin ayyukan su.
Moshood ya ce rundunar ta dade ta na farautar wadannan mutane har Allah ya basu sa’ar cafke su yanzu.
Hannun agogo dai sai kara baya ya ke yi wa Sanata Dino inda al’murran sa sai kara damalmalewa suke yi. Bai dade ba da “mala’iku suka ceto shi” daga tarkon jami’an tsaro kamar yadda ya ce, sannan mutanen mazabar sa sun ce wakilcin tasa ya ishe su haka nan, gashi kuma sun kulla gaba da gwamnan sa na Kogi Yahaya Bello.
Har yanzu Dino bai ce komai akai ba.
Discussion about this post