SANKARAU: Mutum daya ne ya kamu da cutar a Jihar Gombe

0

Jami’in ma’aikatar kiwon lafiyar jihar Gombe David Karatu ya bayyana cewa mutum daya ne kacal cikin mutane shida da ake zaton sun kamu da cutar Sankarau a jihar.

Ya fadi haka ne ranar Alhamis a garin Gombe da ya ke zantawa da kwamitin kawar da cutuka ta ziyarce shi.

Ya ce mutumin da aka tabbatar ya kamu da cutar na samun kula a asibitin gwamnati dake Gombe.

Karatu ya yi kira ga mutane da su gaggauta zuwa asibiti idan basu gamsu da Lafiyar jikin su ba.

Share.

game da Author