2019: Za ayi wa El-Rufai taron dangi

0

Idan dai ba manta ba jihar Kaduna na daga cikin jihohin da suka fada cikin halin kakanikayi na rashin jituwa da a tsakanin mafi yawa daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar APC a kasar nan.

Gwamnan Nasiru El-Rufai, Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hunkuyi duk sun wasa takubban su suna caccakar juna inda kowa ke nuna shine ke da iko da jam’iyyar sannan ya fi Jama’a.

A Kaduna dai abin da kamar wuya domin tabbas, abin bai sake zani ba daga yadda rikicin ya faro tun bayan rantsar da sabuwar gwamnati a jihar a 2015.

Abin kamar zai gyaru a wasu lokutta sai gashi ya sake damalmalewa bayan sanata Suleiman Hunkuyi shima ya raba jiha da gwamna El-Rufai da ya kai ga har kafa sabuwar ofishin jam’iyyar APC yayi a jihar.

Ko da yake hakan bai yi wa gwamnatin jihar dadi ba, hukumar tsara birane na jihar KASUPDA suka zargi wannan gini da kin biyan haraji sannan suka ko rusa ginin.

A haka dai abin kamar za a yi baza ayi ba, komai yanzu ya tsaya cik a jihar musamman ga ‘yan adawar gwamna El-Rufai domin gogan naka maida hankali yayi kacokan zuwa ga yin aiki tukuru a jihar.

Kamar za ayi, baza ayi ba ita kanta kwamitin Tinubu din ta koka da yadda jam’iyyar APC ke gudanar da aikin ta.

Tinubu ya zargi shugaban jam’iyyar John Oyegun da yi wa kwamitin zagon kasa don ganin bata samu nasara ba kan abin da ta sa a gaba.

Shi ko dama can Sanata Shehu Sani, sun dade suna gwabzawa da gwamna El-Rufai. Tun tuni dama ba a ga maciji a tsakanin su.

Alamu dai ya nuna cewa kusan kashi 75 bisa 100 na wadanda suka yi fice a siyasar Kaduna, ba sa tare da gwamna El-Rufai, ga kuma jam’iyyar adawa ta PDP suna gefe suna ta shirya yadda za su yi wa APC kifa daya kwala.

Ma su sharhi sun ce lallai akwai shirin yi wa gwamna El-Rufai taron dangi. kowa zai tattaro makaman yakin sa ya ja daga da gwamnati mai ci domin ganin an ka da ita. Wasu na ganin har jam’iyyar PDP ma an aika mata da goron gaiyyata wannan buki.

Siyasa dai ta matso, kowa kuma ya ja daga, shago cikin su shine zai yi kisa.

Share.

game da Author