Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar wa Majalisar Dinkin Duniya cewa INEC za ta gudanar da sahihin zabe a 2019.
Buhari ya bada wannan tabbacin ne a laokacin da Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed ta gana da shi a Abuja.
Daga nan sai Buhari ya kara yin godiya ga majalisar dangane da kwakkwaran goyon bayan da ta ke bayarwa ga Najeriya.
Amina ta kawo ziyarar kwanki biyu ne a Abuja inda ta gana da Shugaba Buhari da wasu manyan a Lagos.
Wasu daga cikin batutuwan da suka tattauna sun hada da batun zaben 2019 da kuma matsalar tsaro a Arewa-maso-gabas da kuma batun matsalar cinkoson ‘yan gudun hijira.