2019: Buhari ya ki amincewa da kudirin sauya ranakun zabe

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya ki amincewa da sabon kudirin da Majalisar Dattawa ta aika masa nayi wa dokar INEC gyara domin a sauya ranakun zaben 2019.

A cikin wata wasika da ya aika wa Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, Buhari ya bayyana dalilai da dama ciki har da dalilin cewa yin hakan shiga ce cikin gona da hurumin ‘yancin da dokar kasa ta bai wa INEC.

Sauyin da Majalisa ta yi ya maida zaben Majalisar Dattawa da na Tarayya ya zo daga farko, daga nan sai na gwamnoni da na majalisar jihohi a sati na gaba. Sun maida cewa daga karshe ne za a gudanar da zaben shugaban kasa.

Hakan kuwa ya kauce da yadda ya ke a cikin dokar da ta kafa Kukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC.

Dama kuma ‘yan majalisar dattawa karkashin APC sun yi tir da wannan sauyi, wanda suka ce makarkashiya ce ake so a yi wa shugaba Buhari.

Sun kuma zargi Sanata Bukola Saraki da kulla makarkashiyar.

Yanzu dai ya rage wa Majalisa ta amince ko ta ce atabau.

Share.

game da Author