2019: Babu wanda ya isa ya bude min ido -Shugaban INEC

0

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Mahmood Yakubu ya bayyana cewa babu wanda ya isa ya bude masa ido ko ya cika masa ido har ya aikata abin da ba daidai ba dangane aikace-aikacen gudanar da harkokin zabe.

“A zaman yanzu na wuce munzilin da wani zai cika min ido ko ya bude min ido ko ya takura ni da matsin-lambar da zan aikata ba daidai ba.”

Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka ne a cikin wata Tattaunawa Ta Musamman da ya yi kwanan nan da mujallar INTERVIEW da ake bugawa a Abuja.

Ya yi wannan jawabin ne biyo bayan korafe-korafen da wasu ke yi su na nuna damuwar su dangane da batun rajistar zabe da zargin da wasu ‘yan siyasa ke yi cewea INEC ba abin a bai wa amanar gudanar da sahihin zabe ba ce.

A kan haka, sai Yakubu ya ce “ai na wuce munzilin da wani zai cika min ido ko ya bude min ido, ko ya takura ni da matsin-lambar da zan aikata ba daidai ba.”

“Ga tabbacin sahihanci da ingancin zabukan da mu ka gudanar nan a baya, har guda 178. Abin burgewa a nan shi ne kowane bangarorin jam’iyya na zargin mu. To ka ga tunda ba bangare daya ne ke zargin mu ba, ashe hakan na nuni da cewa mu aikin mu ne kawai mu ke yi, ba mu nuna wani bangaranci ko goyon bayan wata jam’iyya ko dan takara.”

Ya ce shi bai taba fuskantar wani kalubale ko matsin-lamba daga Fadar Shugaban Kasa ko daga wani wuri don ya karya doka ya bi son ra’ayin wani ba.

Farfesa Yakubu ya ci gaba da cewa ai ya na sane da cewa gudanar da baragurbin zabe tamkar bin wata turba ce neman wani bala’i ya afka wa kasa. Don haka shi kuma ba zai yadda ya bi wannan turba ba, ba kuma zai yadda wani ya tasa shi a gaba ya ce ya bi turbar ba.

Share.

game da Author