2019: Ana shirin yi wa Saraki ‘Kifa daya Kwala’

0

Wasu sanatoci da gwamnoni da suke in ba Buhari ba rijiya na shirin yi wa Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki tadiyar farad daya a majalisar dattawa.

Sanatocin dai sun kirkiro sabuwar kungiya ce mai suna ‘ Parliamentary Support Group’ PSG a majalisar.

Ita wannan kungiya dai Sanata Adamu Abdullahi ne ke Shugabantar ta sannan cikin dalilan kafa wannan kungiya shine don a hana shirin da Shugaban majalisar Saraki yake yi na yin watsi da shugaba Buhari, majalisa ta sa hannu a kudirin sauya Jerin ranakun zabe da Buhari ya ki saka wa hannu.

Wani jigo a Kungiyar da baya so a fadi sunar sa ya fadi cewa zuwa yanzu Sanatoci 46 sun saka hannu kan wannan tafiya ta su. “Duk da cewa sanatoci 36 ne kawai muke bukata mu hana wannan shiri na su.

“Gwamnoni 20 cikin 24 na APC na tare da mu sannan mun kafa kwamiti a karkashin jagorancin gwamnan Jihar Jigawa domin duba matsalolin da ya kanannade majalisar tarayya.

Ya ce wasu gwamnonin sun umarci sanatocin su su gaggauta sa hannu a wannan tafiya, ” sannan muna bibiyan wasu ‘yan PDP su zo a tafi dasu a wannan tafiya.”

Kungiyar ta ce za ta tabbatar cewa shirin yin amfani da karfin majalisa bai yi tasiri ba wajen ganin an rattaba wa wannan kudiri hannu ta zama doka ba.

Wani dake tare da Kungiyar ya shaida mana cewa wannan tafiya ya wuce maganar kudirin jadawalin shirya zabe, har da ma yadda ake gudanar da shugabancin majalisar.

“An maida mu saniyar ware duk da muna jam’iyya mai rinjaye a majalisa. Kalilan ne suke abin da suka dama a kawai mu sai inda akayi da mu.”

Akwai ganawa da Kwamitin zata yi da wasu gwamnoni da jami’an gwamnati yau Talata a Abuja.

Share.

game da Author