Gwamnan jihar Ondo Oluwarotimi Akeredolu ya bayyana cewa mutane 36 ne suka kamu da cutar zazzabin Lassa a jihar sannan mutane 9 sun rasu cikin su.
Gwamnan ya kara da cewa jihar za ta yi iya kokarin ta don ganin an kawo karshen cutar a jihar. Sannan wadanda suka kamu da cutar na samun kula a asibiti da ke Irrua.
Discussion about this post