ZAZZABIN LASSA: Likitoci sun shiga kasuwannin Osun don wayar wa mata kai

0

Mambobin Kungiyar Likitocin Najeriya reshen jihar Osun sun shiga kasuwannin jihar don wayar da kan mutane musamman mata ‘yan kasuwa game da Zazzabin Lassa, illar da take yi sannan da hanyoyin da za abi don gujewa daga kamuwa da cutar.

Shugaban kungiyar Tokunbo Olajumoke da ya jagoranci likitocin ya ce hakan da suke yi ya zama dole ganin yadda cutar ta yi ajalin wani mutum a asibitin Obafemi Awolowo dake jihar.

Ya ce bayan an Sami rahoton haka asibitin na gwada wasu mutane 40 domin tabbatar da ko sun kamu da cutar ko A’A.

” Dalilin haka ne yasa muka yi tattaki zuwa kasuwanni a Jihar domin wayar da kan mutane musamman mata a harshen da za su fi fahimta domin hana yaduwar cutar.

Share.

game da Author