Gwamnan Jihar Yobe Ibrahim Geidam ya zargi Sojojin Najeriya da yin sakaci har ya yi sanadiyyar yin garkuwa da daliban makarantar sakandare na Dapchi.
” Mako guda da ficewa daga garin Dapchi ne Boko Haram suka kawo wa garin hari sannan har suka iya garkuwa da daliban makarantar sakandare dake Dapchi.
” Irin haka ya taba faruwa a makarantar sakandare na Buni Yadi inda mako guda bayan sojoji sun fice daga garin, Boko Haram suka far wa makarantar suka yanka dalibai 29.
Geidam ya ce dole ya fadi wa mutane gaskiya domin a gaskiya Idan badun sojoji sun fice a garin ba da wannan hari bai auku ba.
” Na yarda a yada yadda na fadi, sai da Sojoji suka fice daga garin mako guda bayan ficewar su ne aka kai wa Dapchi hari sannan aka sace daliban makarantar. Irin dai yadda akayi a 2013, da aka yi wa daliban makarantar Buni-Yadi yankan rago. Shima kwanaki 7 ne da ficewar sojoji.”
Geidam ya bayyana haka da wasu zantukan ne a ziyarar jaje da gwamnan Jihar Barno Kashim Shettima ya kai masa a Damaturu.
Shettima ya jajanta wa gwamnan da iyayen yaran da akayi garkuwa da su.
Daliban makarantar sakandare na Dapchi 110 ne aka tabbatar an sace a makarantar.