Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa mutane kalilan ne suka fito don Kada kuri’ar su a Zaben kananan hukumomi da ake yi a jihar Kano yau.
Kamar yadda bayanai suka nuna, hakan na da nasaba ne da rashin isowar kayan aiki da wuri.
” Wasu wuraren da muka ziyarta mutane kalilan ne suka fito sannan wasu wuraren ma babu mace ko data.
Bayan haka da wakilan jarida suka ziyarci wasu wuraren zabe biyar a karamar hukumar Fagge ta taras cewa wasu mutanen har sun fara tafiya gidajen su saboda rana ta yi sannan ma’aikatan hukumar KANSIEC ba su riga sun kawo kayan zabe ba ko.
” Ni dai na gaji da jiran su domin tun da karfe takwas na safe nake wajen nan amma ka ga har yanzu babu wani ma’aikacin hukumar zaben da ya zo wurin nan.”
Zaben dai kamar za ayi ne kamar ba za a yi ba.
Discussion about this post