Zaben Kano da Katsina ya nuna yadda aka dawo daga rakiyar Buhari, inji PDP

0

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa irin yadda aka yi magudi da kuma jibge jam’ian tsaro a zaben cikie-gurbin da aka ji ranar Asabar a jihar Katsina da zaben kananan hukumomin Kano, sun nuna irin yadda farin jinin Buhari da na jam’iyyar APC ya zube kasa warwas.

PDP ta fitar da wannan bayani ne jiya Lahadi, a ta bakin Sakataren Yada Labaran ta na Kasa, Kola Ologbodiyan, ya kara da cewa an yi zabukan biyu amma an tabka magudi kuru-kuru, an kuma rika cusa tulin kuri’u wanda yin hakan sun maida zaben ya zama wasan yara.

PDP ta ce sakamakon zaben ya nuna irin yadda jam’iyyar mai mulki ba ta da wata kimar iya gudadnar da sahihin zabe.

PDP ta ci gaba da cewa yadda APC ta amfani da karfin jami’an tsaro domin ta samu fifikon yawan kuri’u a zaben cike-gurbin kananan hukumomin Dutsi da Mashi na JIhar Katsina, ya nuna irin yadda Shugaba Buhari da jam’iyyar sa ba su da sauran farin –jini ko a jihar sa ko kuma mazabar sa.

“Da APC na da farin jini a Yankin Daura, da ta yi wa PDP mummunan kaye a jihar Katsina. Amma ku dubi duk da irin magudin da su ka yi, har ta samu kuri’a 30, 719, sai da APC ta samu kuri’a sama da dubu 22,000.

PDP ta gargadi APC cewa ba za a amince jam’iyya mai mulki su yi rin wannan tafka magudi a zaben 2019 ba. Ta na mai karawa da cewa ya kamata ta bari soyayyar da ta ke cewa ana yi wa Buhari, to a bari a ga kaunar da soyayyar a cikin akwatunan kada kuri’a, ba wai sai an yi magudi ba.

Share.

game da Author