ZABEN KANANAN HUKUMOMIN KANO: Wane darasi APC ta koya wa sauran jam’iyyu?

0

Zaben Shugabannin Kananan Hukumomin Jihar Kano da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, ya zo ya wuce, amma fa ya bar baya da kura. Baya ga nasarar da aka bayyana cewa jam’iyyyar APC ce ta lashe zaben na dukkan kananan hukumomin 44, tuni a washegarin zabe, a tsakar dare Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya rantsar da Shugabannin Kananan Hukumomin, su kuma suka rantsar da kansilolin su kakaf.

Sai dai tun ma kafin a kammala zaben aka rika watsa hotunan kananan yara da aka yi zargin sun dangwala kuri’a birjik. Dama kuma an samu babbar matsala a zaben, domin mafi yawan wurare sai bayan la’asar aka aka kai musu kayan aiki.

Su kan su malaman zaben ba su isa wurare da wuri ba. Ba gamegarin jama’a ne kadai su ka yi korafin cewa an tafka magudi a zaben ba. Su kan su kungiyoyin sa-ido irin su CITAD, sun tabbatar da cewa zaben ba na kwarai ba ne, an tafka magudi, kuma sun hakkake cewa kananan yara sun yi zabe.

Da daman a cewa ko a lokacin PDP ba a taba tafka abin kunya kamar yadda aka yi a zaben kananan hukumomin Kano ba.

Ganin yadda ake ta Allah-wadai da yadda Hukumar Zabe ta Jihar Kano ta gudanar da zaben, a jiya Talata sai Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta yi gaggawar fitowa ta nisanta kan ta da zaben da aka gudanar a jihar Kano.

INEC ta tsinkayar da jama’a cewa ya kamata fa kula, ba Hukumar Zabe ta Kasa ce ta shirya zaben ba. Zabe ne da jihar Kano ta shirya karkashin hukumar zabe ta jihar.

INEC ta roki jama’a da su daina kallon irin yadda aka yi zaben Kano sun a dora shakku kan yadda INEC za ta gudanar da zabukan da ke gabanta na kasa baki daya nan da shekara daya daidai.

Hukumar ta ci gaba da cewa ita ma ta shaida hotunan kananan yara da aka rika nunawa, an dauke su ne a lokacin da ake kada kuri’a a zaben kananan hukumomin Kano.

To, sai dai kuma wata sabuwa, ita ce hirar da manema labarai su ka shi gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje a Fadar Shugaban Kasa, jiya Talata, inda ya tsaya kai da fata cewa sahihin zabe aka yi a Kano, ba a yi magudi ba.

Da ya ke magana kan zargin yadda kananan yara suka rika dangwala kuri’a kuru-kuru, Ganduje bai dora wa kowa laifi ba, sai tsohon ubangidan sa, Sanata Kwankwaso. Ya ce shi ne da mutanen sa suka kulla wannan sharrin cewa kananan yara sun yi zabe.

Ganduje ya ci gaba da cewa saboda Kwankwaso da jama’ar sa sun kasa fitowa zaben ne shi ya sa suka cika kafafen sadarwa na soshiyal midiya da farfaganda domin su damalmala lissafi, a ga kamar an yi magudi.

Zaben ya zo daidai da lokacin da ake kakkausan rashin jituwa tsakanin Kwankwasiyya da Gandujiyya a Kano da ma kasa baki daya. Har ila yau, zaben ya zo daidai da sati daya bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Bola Tinubu ya sasanta bangarorin da ba su zama a karkashin inuwa daya a cikin jam’iyyar APC.

Yayin da ake kallon kamar Ganduje ba ya nuna biyayya ga shugaban kasa, wajen tsuke bakin sa ya yi shiru, tunda an nada Tinubu ya sasanta, sai ma kara sakin-baki ya ke yi ya na ci kaga da kasassabar da ke kara kawo baraka a cikin jam’iyyar APC a Kano.

Abangaren Kwankwaso ma, duk wanda ya furta bakin sa zai ce wani abu, sai dai ka ji ya ce “babu sassauci.”

Da yawa na ganin cewa kwamitin Tinubu ba zai yi wani tasiri a Kano ba, domin sai da Buhari ya gama kware wa Kwankwaso baya, ya dauki Ganduje da Sanata Lado ya goya, sannan ya nemi a sasanta Kwankwaso da Ganduje.

Masu lura da al’amurran siyasar Kano na ganin cewa a karshe idan ba a tashi tsaye ba, to za a iya yin biyu-babu ko ma uku-babu – wato Buhari da Ganduje da Kwankwaso duk su rasa jihar Kano, ko kuma Buhari da Ganduje su rasa.

Hakan zai iya faruwa idan dimbin magoya bayan Kawankwaso su ka ki jefa wa Ganduje kuri’ar su, kuma su ka ki jefa wa Buhari a zaben shugaban kasa.

Magance afkuwar haka kamar yadda wasu ke gani, shi ne Buhari ya balle zanin goyo, ya ajiye Lado, ya dauki Kwankwaso ya goya. Sannan ya ja kunne Gwamna Ganduje, ya nuna masa jama’ar Kano ya ke mulki ba gwamnatin Kato-da-gora b ace.

Hakan zai sanyaya mabiya Kwankwasiyya a Kano da ma kasa baki daya.


Amma idan aka bari Kwankwaso ya fusata, to zai iya yi wa APC sakiyar da babu ruwa.

Shi kuwa zaben kananan hukumomi, ya zo kuma ya wuce. Amma tabbas ya rage wa APC karsashin adalcin da ake kallo ta zo ta shimfida a kasar nan.

Shin a haka za a tafi, ko kuwa za a maka hukumar zaben jihar Kano kotu domin a sake zaben? Mu na ji, mu na gani, mu na kuma saurare.

Share.

game da Author