Za mu ba mata fom din takara kyauta a Kaduna – Jam’iyyar PDP

0

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa za ta ba duk macen da za tayi takarar kujeran kansila da na shugaban karamar Hukuma a zaben kananan hukumomi mai zuwa da za a yi a Kaduna fom kyauta.

PDP ta ce mai neman takarar kansila zai siya fom din nuna son yin takara naira N5000 sannan kudin fom naira N30,000.

Ciyaman kuma zai siya fom din nuna son yin takara naira N25,000 sannan kudin fom kuma N100,000.

Hukumar zabe na Jihar Kaduna ta tsaida ranar 12 ga watan Mayu domin gudanar da Zaben kananan hukumomi a Jihar.

Share.

game da Author