Za a yi gangamin magoya bayan Buhari milyan daya a jihar Neja

0

Wata kungiya mai goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari, ta bayyana cewa reshen ta jihar Neja zata gudanar da taron gangamin mutane miliyan daya a Minna, babban birnin jihar.

Shugaban Kungiyar Buhari Campaign Organisation na Arewa ta Tsakiya ne, Ubale Kagara ya bayyana haka a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN.

Ya ce kungiyar su za ta ci gaba da yayata abubuwan alherin da Shugaba Muhammadu Buhari ta gudanar daga hawan sa mulki zawa yau.

Sannan kuma ya yi bayanin cewa za su nuna namijin kokari wajen sake zaben Buhari a zabe na 2019.

Kagara ya ci gaba da cewa irin kokarin da Buhari ya yi wajen yaki da rashawa, Boko Haram, da inganta tsaro da tattalin arziki, sun isa a sake zaben sa domin ya ci gaba da karasa ayyukan da ya faro.

Share.

game da Author