Za a samar da magungunan kawar da yunwa a Kaduna

0

Jami’in hukumar kula da yaran dake fama da yunwa na jihar Kaduna Shehu Makarfi ya bayyana cewa gwamnan jihar Nasir El-Rufa’I ya bada umurin samar da magungunanar kawar da yuwa wanda ake kira da ‘Ready to Use Therapeutic Food RUTF’ ga yara kanana masu fama da irin wannan matsalar a jihar.

Ya sanar da haka ne wa manema labarai bayan sun kammal tattaunawa game da shirin da aka yi a Zariya, jihar Kaduna ranar Lahadi.

Makarfi ya ce gwamnan jihar Kaduna ya bada wannan umurni ne domin gujewa karancin magungunan nan gaba wanda hakan ka iya dawo da hannun agogo baya wa shirin.

Ya ce domin tabbatar da haka El-Rufa’I ya umarci kowace karamar hukuma a jihar ta bada gudunmawar Naira 500,000 duk wata sannan ya kara tabbatar da cewa gwamnati za ta hukunta duk ma’aikacin da aka kama da laifin wawushe wannan kudade.

Share.

game da Author