Za a horas da matasan jihar Kaduna dabarun iya shugabanci

0

Gwamnatin jihar Kaduna ta tsara shirin horas da matasa dabarun iya shugabanci da ta yi wa suna ‘Kashim Ibrahim Fellows Programme’.

Gwamnati ta ce ta yi haka ne domin samar da matasan da za su kawo ci gaba a jihar da kasa Najeriya ta hanyar iya shugabanci.

Bayyanai sun nuna cewa shirin za ta horas da matasa masu shekaru tsakanin 25 zuwa 35 na tsawon shekara daya.

Matasan za su sami horo ne kan yadda ake tsara kudirorin da za su kawo ci gaba, kalubalen da za su iya fuskanta da yadda za su iya shawo kan su da makamantan haka. Sannan za a biya matasan albashi kamar yadda masu taimakawa gwamna suke karba tare da samar musu wajen zama.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I ya ce suna sa ran bayan kammala horas da matasan za su koma wajen aiyukan su ko kuma inda aka basu aiki domin nuna abin da suka koya.

Za a fara shirin a watan Yuni 2018.

Share.

game da Author