‘Yar sanda daya ce Boko Haram tayi garkuwa da, ba 10 ba – Kwamishinan ‘Yan sanda

0

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Barno Damian Chukwu ya bayyana cewa cikin mutane 13 da Boko Haram ta sako daya ce kawai ma’aikaciyar su, wato ‘yar sanda.

Ya sanar da haka a yammacin Litini da yake zantawa da manema labarai a ofishin sa.

Idan ba a manta ba a karshen makon da ya gabata ne fadar shugaban kasa ta sanar cewa Boko Haram sun sako wadannan mutane wanda cikin su akwai malamai uku na jami’ar Maiduguri da matan ‘yan sanda 10.

Chukwu ya kuma kara tabbatar wa manema labarai maganar da ya yi a wancan lokaci cewa ‘yar sanda daya ce aka sace sauran matan ‘yan sanda ne da akayi garkuwa dasu su a dajin a kauyukan su.

Ya karyata rahoton gidajen jaridu cewa wai ‘yan sanda 10 ne Boko Haram ta sace. ” Yar sandan da aka sace sunan ta Fatsumatu Haruna.”

” Abin da na fada bara shine ma’aikaciyar mu Fatsuma Haruna na cikin mata 10 da Boko Haram ta sace yayin da suke hanyar zuwa kauyen Lassa domin birne gawan kawar su amma ban ce Boko Haram ta kama ma’aikatan ‘yan sanda mata 10 ba.”

Share.

game da Author