Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana cewa ‘yan siyasa su ne babbar barazana da dorewa ko kuma ingancin dimokradiyya a Najeriya.
Jega, wanda shi ne ya shirya zaben 2011 da na 2015, yay i wannan bayani ne a ranar Alhamis, yayin da ya ke jawabi a wurin wata lacca mai take: “Shin Dimokradiyyar Najeriya Na Fuskantar Barazana Kuwa?”
Laccar dai wata kungiyar matasa ce mai rajin kawo ci gaba ta shirya taron, wato, YIAGA, a Abuja.
A ta bakin Jega, babbar barazana ga dimokradiyya shi ne yadda ‘yan siyasa ke yi wa siyasa da dimokradiyya tukin ganganci, wanda hakan ke lalatawa da dagula tafarkin ci gaban kasa.
Ya ce, “Kamar sauran kasashe, ita ma Najeriya na fuskantar barazana ga tubalaye da ginshikan kafa dimokradiyya din ta. Ya zama dole mu gano wadannan barazanar domin mu gaggauta magance su.
“Akwai kuma bukatar mu wayar wa mutanen mu kai a kauyuka da garuruwa cewa su shiga cikin harkokin zabe a dama sa su, kuma mu tabbatar ba mu koma kan yadda ake karfa-karfa ba, wadda hakan ne ya maida mu baya sosai.
“Alamomin yadda su ke illata dimokradiyya ai ga su nan a fili mu na kallo, ga shi kuma a halin yanzu kasar ta mu na fuskantar matsalolin tsaro birjik.
Daga nan sai Jega ya shawarci ‘yan Nijeriya da su rika zaben mutane nagari da za su yi musu kyakkyawan wakilci kuma za su nuna kishin talakawa.
Babban Daraktan YIAGA, Solomon Itodo, ya ce gas hi dai yanzu saura kwanaki 358 a gudabar da zaben 2019, akwai matukar bukatar ‘yan Najeriya su zana wa kan su sabuwar taswirar da su ke so kasar ta kasance idan an sake sabon lale.