‘Yan Najeriya Miliyan 144 su ka mallaki wayar salula – NCC

0

Hukumar Sadarwa ta Kasa, NCC, ta bayyana cewa akalla akwai mutane miliyan 144, 631,678 masu amfani da wayar salula.

Wannan adadi kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito, na nufin yawan layukan wayoyin hannun da ake amfani da su a Najeriya sun wuce milyan 144 kenan.

Kafin adadin ya kai haka a cikin watan Disamba, a cikin watan Nuwamba adadin ya na miliyan 141,900.405 ne, wato an samu karin mili yan 2,731,273 kenan.

Share.

game da Author