‘YAN MATAN #Dapchi: Tawagar gwamnatin tarayya ta isa garin Damaturu a karo na biyu

0

Tawagar wanda ya hada da ministan yada labarai, Lai Mohammed da Ministan harkokin ciki gida Abdulrahman Dambazau sun isa garin ne a wata jirgi sama mai saukar Angulu da misalin 12n Rana.

Iyayen daliban makarantar sakandare ta Dapchi a jihar Yobe, sun fitar da jerin sunayen dalibai mata 195 wadanda suke ce sun tabbatar an gudu da su jiya Asabar.

Iyayen sun bayyana haka ta bakin shugaban wata kungiya da suka kafa, ta iyayen da Boko Haram suka sace wa ‘ya’ya, sun ce maganar gaskiya duk labaran shaci-fadi kawai jamai’an tsaro ke kai wa gwamnan jihar Yobe.

Wannan shine karo na biyu da tawagar Gwamnatin tarayya ke kai ziyara garin na Damaturu.

Share.

game da Author