‘YAN MATAN #DAPCHI: Kada gwamna Geidam ya dora mana laifi, Inji Sojojin Najeriya

0

Hukumomin Sojojin Najeriya sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa duk da garin Dapchi na cikin kananan hukumomi uku da Boko Haram suka yi kamari a jihar Yobe, ba a girke dakarun sojoji a garin ba a baya har sai bayan harin da aka kai aka sace dalibai na sakandaren garin a makon da ya gabata.

Gwamnan Jihar Yobe, Ibrahim Geidam ya shaida cewa sojoji ne za a dora wa laifin sace daliban mata 110, kusan shekaru hudu bayan sace wasu 276 a makarantar Chibok ta jihar Barno.

Ya ce ya dora laifin ne kan hukumar tsaro da ta janye sojoji daga Dapchi, “saboda an kai harin ne mako daya kacal bayan janye sojojin daga can. Amma kafin sannan ai garin Dapchi zaune ake lafiya.”

Wadannan kamalai na gwamnan ba su yi wa hukumar sojoji dadi ba, domin sun maida martani inda kakakin yada labaran su ya ce gwamnan dai ya na da wani mugun nufi ne kawai.

“Kafin a kai hari a Dapchi dai babu sojoji a can. Shi ma gwamnan ya san cewa babu sojoji a garin.” Haka Burgediya Janar John Agim ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Agim ya ce inda sojoji su ke a yankin tsakanin su da Dapchi zai kai kilomita 30. Amma bai fadi sunan wurin ba.

Daga nan sai ya ce ya na so gwamnan da ‘yan Najeriya su san cewa sojoji ba su iya kare ilahirin makarantun jihar Yobe da Barno gaba daya ba.

Sai dai kuma tun a lokacin da gwamna da ‘yan sanda ke dawurwura, tuni Hon. Goni Bukar dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar da aka sace daliban ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an tabbatar masa ko tantama babu cewa Boko Haram sun gudu da dalibai da dama.

Share.

game da Author