Rundunar Sojojin Najeriya sun bayyana cewa sun samu gagarimar nasarar ragargaza babban sansanin Boko Haram a Dajin Sambisa.
Sanarwar da suka fitar a ranar Laraba, ta ce babban sansanin da Boko Haram ke shirya dabarun kai harin sari-ka-noke ce su ka ragargaza.
Kakakin Yada Labaran Sojoji, Sani Usman, ne bayyana haka a Maiduguri a ranar Laraba. Ya na mai kari da cewa zaratan sojojin ‘Opretion Lafiya Dole’ a karkashin ‘Operation Deep Punch’, su ka kai wannan farmakin tare da samun gagarimar nasara.
Burgediya Janar Usaman, ya ce daga cikin kayan da aka kwato sun hada da tankar yaki, tulin bindigogi, albarusai, littafan addini, tukwanen gas da takin zamani, wanda su ke hadawa su na shirya bama-bamai.
Sannan ya ce an kuma lalata wa Boko Haram motocin daukar mahara har guda bakwai, wasu motoci da dama, babura da kuma bukkokin da su ke kwana a ciki da dama.
Ya ce an kai harin ne a ranar Talata, 30 Ga Janairu, 2018.