Yadda jirgin kasa ya markade wani matashi a Abuja

0

Wani magidanci mai suna Francis Idoko, ma’aikacin Hukumar Kula Jami’o’i ta Kasa, ya bayyana yadda ya i wa dan sa ganin karshe, wanda jirgin kasa ya markade a kusa da Kubwa, a Abuja, shekaranjiya Juma’a da safe.

Da ya ke magana da Kamfanin Dillancin labarai na Najeriya, Idoko ya ce dan sa mai suna Paul ya shirya tafiya wurin aiki kamar yadda shi ma ya shirya zai fita.

“Ya shigo har cikin daki na ya gaishe ni, a lokacin mahaifiyar sa na kwance ba ta tashi ba, sai na tambaye ta idan ta na da N50 ta ba ni na hau okada daga can na hau mota kyauta zuwa wurin aiki.

“Nan take sai Paul ya dauko N50 ya ba ni, na karba, na yi godiya na fita.
“9:30 na safe bayan na je ofis, sai wani aboki na ya kira ni, ya ce na kira shi, akwai wata maganar gaggawa da zai sanar da ni.

“Ina kiran sa sai ce min ya yi ai da na ya mutu. Na ce kai, ba zai yiwu ba, domin a safiyar nan fa shi ne ma ya ba ni naira N50 na hau babur.

“Daga nan kuma sai wani makwauci na mai suna Hassan ya kira ni, ya kara shaida min. Nan take na kira mata ta na shaida mata, a lokacin ita da wata ‘ya ta su na falo sun a kallon TV.

Idoko ya ce jirgin kasan markade dan sa Paul ya yi, har sai da aka rika tattaro naman jikin sa, aka kwaso daga kan kwangirin jirgin kasa.

Ya ce ya garzaya domin ya je wurin ‘yan sanda a kai gawar dan sa matuware, amma ‘yan sanda su ka ce ai ba su da wannan ikon, ba aikin su ba ne.

“Daga karshe dai mu ka je ofishin ‘yan sanda na Kubwa, aka kai shi asibiti, sannan daga baya jama’a suka taru muka rufe gawar sa.

Yayin da wani abokin sa mai suna Sunday Garba ya bayyana wa NAN cewa tare suka fita, har zuwa yayin da jirgi ya zo zai wuce. Shi ya ki tsallakawa, amma ya nemi Paul ya rasa. Sai da ya kira lambar sa, ya ji ta a kashe, daga baya sai ya ga rigar sa a kan kwangiri, can kuma ga naman jikin sa a markade.

Kakakin Jami’an ‘Yan Sandan Abuja ya ce bai samu rahoton hadarin ba, yayin da Idoko ya ce har yanzu ko jaje hukumar jiragen kasa ba ta je ta yi musu ba.

Share.

game da Author