Sakataren yada labarai na jihar Kebbi, Abubakar Dakingari ya bayyana cewa mutane 12 sun bace sannan wasu shida sun rasa rayukansu sanadiyyar karon da wasu jiragen ruwa biyu suka yi a karamar hukumar Shanga jihar Kebbi.
Dakingari ya ce hadarin ya auku ne a tekun kauyen Barikin Sakace dake karamar hukumar Shanga daidai wasu ‘yan kasuwa 78 da kayansu ke hanyar dawowa gidajen su da misalin karfe takwas na yamman ranar bayan cin kasuwa.
Daga karshe Dakingari ya ce domin hana maimaicin irin haka gwamnan jihar Atiku Bagudu ya kafa dokar hana tafiyar dare a jiragen ruwa sannan ya yi kira ga masu unguwani, shugabanin kanannan hukumomi da hukumomin gwamnati da su taimaka wajen ganin mutane sun yi wa dokar biyayya.