WASIKAR BABANGIDA: Yadda kalaman IBB su ka yi harshen-damo

0

A jiya ne kafafen yada labaran Najeriya suka fada cikin rudani, sakamakon kalamai mabambanta da aka ruwaito cewa sun fito daga bakin tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Babangida.

Kalami na farko, wanda kakakin yada labaran sa, Kassim Afegbua ya fitar, ya bayyana takaicin da Babangida ke ji dangane da rashin salon iya mulkin Shugaba Muhammdu Buhari, inda a ciki har ya nemi ya hakura kada ya sake tsayawa takara a 2019.

Babangida ya nemi Buhari ya hakura ya bar wa masu sauran jini a jika.

Buhari wanda ya shugabanci kasar nan tsakanin 1985 zuwa 1993, ya ce a yanzu lokacin ya yi da dattawa za su janye jikin su daga shugabanci, su kyale masu jini a jika su shiga gaba. Ya ce hakan zai sa kasar nan ta rika yin gogayya da kasashen da a yanzu su ka tsere mata fintinkau.

Babangida wanda ya yi mulki bayan hambarar da Buhari a lokacin da ya ke shugaban kasa na mulkin soja, a yanzu ya na da shekaru 76.

Sai dai kuma jim kadan bayan fitar da sanarwar, kasar nan ta dauki dumama inda aka rika yayata labarin tare da yin sharhi.

Ana cikin haka kuma sai ga wata wasika ta fito, wadda ta karyata takarfdar farko. Amma ita wannan jawabin bai yi tsawo sosai ba.

Bayani na biyu ya ce takardar da Afegbua ya fitar ba gaskiya ba ce, kuma ba Babangida din ne ya sa mata hannu ko ya rubuta ta ba.

“Ina so na sanar da jama’a cewa a matsayi na na tsohon shugaban kasa kuma dattijon da kasar nan ke mutuntawa, ina da kusanci da damar da zan iya ganawa da shugaban kasa ko gwamnati kai tsaye, ba sai na shiga kafafen yada labarai ina maganganun da za su haifar da rudu ba.”

Wannan bayani na biyu, Babangida ne da kansa ya sa masa hannu.

Sai dai kuma Babangida ya ce yayi amanna har yanzu tsarin jam’iyyu biyu a kasar nan shi ne mafi alfanu.

Shi ma Afegbua sai ya garzaya a gidan talabijin na Channels inda ya kara tabbatar da cewa wasikar farko da ya fitar daga Babangida ta ke.

Ya kara da cewa har da Babangida aka yi zaman da ya rubuta takardar, har ma ya na kawo gyare-gyare a cikin wasikar ya na cewa a cire kaza a kara kaza kafin shi Afegbua ya fitar da wasikar a ranar Lahadi da rana.

Share.

game da Author