WASANNI: Sergio Ramos ya buga wasa 550 a REAL MADRID

0

Mai tsaron bayan Real Madrid, Sergio Ramos, ya buga wasa na 550 a kungiyar tun bayan da aka sayo shi daga kungiyar Sevilla, ita ma da ke kasar Spain.

Wasan da kungiyar ta yi a jiya Laraba ne wasan sa na cikon 550, inda a nan ma ya samu nasarar jefa kwallo a raga.

A tsawon wadannan wasanni da ya yi, ya taka muhimmiyar rawa wajen jefa kwallaye a ragar abokan karawa har ya ci kwallaye 72, duk kuwa da cewa aikin sa shi ne tsaron baya.

Wasu da suka fi shi yawan buga wasanni a kungiyar Real Madrid, sun hada da Raul Gonzalez wanda ya buga wasa sau 741, sai kuma Iker Casillas, tsohon mai tsaron gidan kungiyar da ya buga sau 725, da sauran wasu kamar ‘yan wasa shida.

Ramos shi ne kaftin na kungiyar, kuma shi ne kaftin na kungiyar kwallon kafa ta kasar Spain.

Share.

game da Author