Wani magidanci mai suna Stephen Nnadiogo
Ya kashe ‘ya’yan sa na kan sa su hudu duka da kanwar matar sa da take zaune da su a Jihar Anambra.
Shi dai Stephen dama yana fama da ciwon hauka, sai dai bayanai sun nuna cewa kafin ya aikata haka ya sami sauki.
Wata hadima a gidan ta ce ta kubuta me bayan arcewa da ta yi da gudu a lokacin da yake aikata hakan.
Sai dai kuma duk wannan abu ya faru ne a lokacin da mai dakin sa bata gidan.
Jami’in ‘yan sanda Stephen Nnadiogo ya bayyana cewa an fara gudanar da bincike don gano ainihin abinda ya faru.
Discussion about this post