Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Muhammada Bello, ya bayyana rashin jin dadin sa kan yadda ake harkallar cinikin filaye da gonaki a yankunan Abuja.
Ministan ya yi kakkausan gargadi ga kowa ya dakatar da sayen fili ko gona wadanda aka mallaka wa yankunan Abuja, har sai an kammala sauran ka’idojin da ba a kai ga kammalawa tukunna.
Babban Sakataren FCT, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Raba Filaye, Chinyeaka Ohaaa ya yi wannan bayani a wani taron da kwamitin ya yi a Abuja.
Ya kara da cewa ya zama tilas a yi wannan bayani domin a rage yadda masu bumburutun filaye ke ci gaba da harkallar su a cikin yankunan kananan hukumomin Abuja. Ya ce su na yawan zambatar masu neman sayen filaye ido rufe.
Ohaa ya yanko wata aya daga cikin kundin dokar kasa mai lamba 297 (2) daga kundin tsarin mulki na 1999, wanda ke nuna cewa gaba dayan filin yankin Abuja da kewaye, mai murabba’in kilomita 8,000, duk ya na karkashin kulawar Ministan Abuja ne, shi aka dora wa alhakin kulawa da shi.
Sai ya ce amma ya lura duk da an dakatar da yankunan Abuja daga sayar da filaye, tun a cikin 2006, har yanzu ana ci gaba da wannan harkallar.
A karshe ya yi kira ga duk wanda ya san an mallaka masa fili ta halastacciyar hanya, to ya garzayo ya karbi satifiket na mallaka ko kuma takardar mallaka ga wanda bai kai ga biyan kudin satifiket ba.
Discussion about this post