Hukumar UNDP ta bayyana cewa za ta tallafawa ‘yan gudun hijiran dake zama a kauyen Ngwom, karamar hukumar Mafa jihar Barno da makarantar firamare, gidajen zama, shaguna da cibiyar kiwon lafiya.
Jami’in hukumar Samuel Bwalya wanda ya sanar da haka ya ce Kauyen Ngwom na daya daga cikin kauyukan jihar Barno da suka yi fama da hare-haren Boko Haram tun daga shekarar 2014.
Bwalya ya ce hukumar za ta danka wa mazauna wannan kauye ginannun gidajen zama 292 daga cikin 300 da ta yi alkawarin ginawa, makarantar Firamare, asibiti, shaguna 288 da manyan shaguna 20 ranar 28 ga watan Faburairu.
” Sanadiyyar wannan hidima da muka sa a gaba mutanen kauyen sun sami aikin yi.”
Ya kuma kara da cewa hukumar ta rabawa manoman kauyen da suka kai 550 kayan noma sannan za su samar da tsaro a kauyen domin kare rayuwa da dukiyoyin mutanen.
A karshe Bwalya ya ce sun yi haka ne domin inganta rayuwar mutanen kauyen domin su sami damar ci gaba da rayuwar su kamar da.
Discussion about this post