Tsohon Mataimakin Sufeto Janar ya goyi bayan a kafa ‘yan sandan jihohi

0

Tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Raimi Odofin, ya bayyana cewa Najeriya ta kai munzilin da za a ce kowace jihar na da nata ‘yan sandan jiha daban, bayan jami’an ‘yan sanda na kasa.

Odofin ya bayyana haka ne yau Alhamis, yayin da ya ke ganawa da Kamfanin Dillancin Labarai, NAN. Ya ce matsawar aka yi haka, to za a karfafa matakan kalubalantar matsalar tsaro a kasar nan.

Ya ci gaba da cewa ba zai yiwu a koda yaushe mu tsaya wuri daya ba mu na kafa hujja da cewa wai gwamnoni za su iya maida wadannan jami’an tsaro su zama karnukan farautar su ba.

Amma kuma ya yi kira da cewa kada gwamnonin su kafa ‘yan sandan da nufin cizgunawa, musgunawa ko kuma maida su karnukan farautar siyasa.

A karshe, tsohon sufeto janar din ya shawarci jihohi cewa duk gwamnan da ke da karfin daukar nauyin hidimar ‘yan sandan, to shi ne kadai zai kafa.

Share.

game da Author