Rahoton da Global Wealth Review ya wallafa, ya tabbatar da yadda attajirai da dama ke ta gudu daga Lagos, su na karkata jarin su zuwa Aukland da kuma Dubai.
Hakan kuwa ya biyo bayan yawan haraji da kuma tsananta shi da gwamnatin jihar Lagos da tarayya ke yi a kan masu masana’antu da ‘yan kasuwa da kuma masu zuba jari.
Har ila yau, an kwatanta Lagos da Birnin London, inda a can ma aka gano cewa yinkurin da kasar ta yi na ballewa daga Kungiyar Tarayyar Turai, wato Brexit, ya haifar da manyan masu jari har 5,000 sun janye jarin su daga Ingila, su ka karkata zuwa Aukland da Dubai.
Sai dai kuma an nuna cewa daga baya guda 1,000 sun dawo, amma har yau 4,000 ba su maida jarin na su a birnin Landan ba.
Tun bayan hawan gwamnatin APC ta bayyana cewa za ta bada karfi wajen dora wa jama’a haraji, domin a rika samun kudin tafiyar da gwamnati da ayyukan ta, sannan kuma a rage yawan dogaro da fetur.