TSAKANIN BUHARI, GANDUJE, KWANKWASO: Wa zai riga rana faduwa a Kano?

0

BUHARI: Ya samu matsala a Kano. Akwai rashin samar da manyan ayyukan gwamnatin tarayya kamar yadda aka rika yi a Legas. Ya rasa dimbin mabiya Kwankwasiyya. Taron da Ganduje ya yi tare da masu dauke da muggan makamai ya janyo jama’a na nuna alhini ga Kwankwaso, sannan kuma zaben Kananan Hukumomin Kano ya kara rage wa APC kwarjini a idon jama’a.

GANDUJE: Bai kai Kwankwaso yawan magoya baya ba. Ya rasa dimbin magoya bayan Kwankwaso, wadanda ba za su zabe shi ba, sai dai su zabi abokin hamayyar sa. Rigimar sa da Kwankwaso ta karya karfin APC. Gangamin da ya shirya dauke da makamai ya kara shafa masa kashin-kaji a rigar siyasar sa. Sannan kuma Kanawa ba za su yi “SAK’’ ba.

KWANKWASO: Ganduje zai iya amfani da karfin gwamnati ya hana shi katabus a wurin zabe. Kwankwaso ba ya zuwa kananan hukumomi da mazabun da ke karkashin wakilcin sa. Ba ya zama a Kano ana kulla kitimirmirar siyasa da shi da magoya bayan sa. Fada da Buhari da Ganduje shi kadai ba karamar kokawa ba ce.

Share.

game da Author