Tinubu ya maida wa Obasanjo martani kan wasikar da ya yi wa Buhari

0

Tsohon gwamnan jihar Legas, kuma jigo a jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya bayyana cewa wasikar da Obasanjo yayi wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari, siyasa ce kawai.

Tinubu ya fadi haka ne da yake zantawa da manema labarai a garin Owerri, a hanyar sa ta zuwa jihar Anambra wajen jana’izar tson mataimakin shugaban kasa Alex Ekweme.

Ya ce Obasanjo yana da dama ya gana da Buhari yadda yake so a matsayin sa na tsohon shugaban kasa sannan ogan sa a aikin soja.

“ Obasanjo da Buhari sun fi kusa, ba tun yanzu ba. Tsoffin Sojoji ne, sun san juna. Obasanjo na da hanyoyi dabam-dabam da zai gana da Buhari su tattauna kan koma menene. Kuma fa ogan Buhari ne a lokacin aikin sun na Soja. Sun hadu a taron kungiyar kasashen Afrika da akayi a kasar Ethiopia. Duka suna tare.”

Da aka tambaye shi game da sabuwar kungiyar da Obasanjo ya kafa, Tinubu, y ace duk wani dan kasa na da ikon kafa kungiya domin doka ta bashi wannan dama.

Share.

game da Author