TARZOMA: An rufe kwalejin ilimi na Gindiri

0

Kwalejin ilimi dake Gindiri, karamar hukumar Mangu jihar Filato ta rufe karatu a makarantar sakamakon rikicin da daliban makarantar su ka tada a yau Alhamis.

Kakakin kwalejin Elizabeth Aboreng ta shaida wa PREMIUM TIMES ta wayan cewa sanadiyyar wannan rikicin daliban makarantar sun kona musu asibiti, motocin daukan marasa lafiya biyu da motocin ma’aikatan makarantan guda shida.

” Jami’an tsaron da muke da su sun kasa kwantar da rikicin sannan ko kafin ‘yan sanda su zo daliban su riga sun yi barnar da suka yi.Dalilin haka ya sa muka dakatar da karatu zuwa dan wani lokaci domin hana daliban ci gaba da banar da suka fara.”

Bayanai sun nuna cewa daliban makarantar sun tada wannan rikici ne saboda rashin ba su katin shaida da shine kadai zai iya ba dalibi damar rubuta jarabawa.

Wani dalibi ya shaida mana cewa ” Misali sannin kowa ne cewa dalibai na biyan wasu ‘yan kudade bayan ainihin kudin makarantar da ake biya wanda ya hada da kudin magani amma sai aka wayi gari idan ka je asibiti sai ka biya makudan kudade kamar baka taba biyan wasu kudade ba da farko.”

Dalibin wanda baya so a fadi sunnan sa ya ce babu yadda za su iya da makarantar musamman yadda babu kungiyar dalibai a makarantar.

” Sanadiyyar haka ya sa muka rasa wakilin da zai iya kai kukan mu ga hukumar makarantar domin a biya mana bukatun mu.”

Share.

game da Author