Tanko ya shirga wa JAMB karya wai katin jarabawa na miliyan 23 sun kone a hadarin mota

0

Bayan labarin hadiyan miliyan 36 da maciji ya yi na kudaden hukumar JAMB a jihar Benuwai wani ma’aikacin hukumar a jihar Nasarawa ya bada nashi labarin tashin tantabaru kan yadda kudaden hukumar da ta kai Naira miliyan 23 suka bace.

Jami’in hukumar na jihar Nasarawa, Labaran Tanko ya bayyana wa kwamitin da aka kafa don binciken badakalar siyar da katin duba sakamakon jarabawa na daliban da suka rubuta cewa shi na sa katin da kudin su yakai naira miliyan 23 ya konewa suka yi a hadarin mota da yayi a hanyar sa na zuwa Abuja.

” Ina wa Allah godiya na tsira da rai na don ko da ba haka ba yanzu sai dai katin duba jarabawar duk sun kone.

Bayan ya bayyana haka ne kwamitin ta dakatar da ci gaba da sauraren Tanko. Daga baya sai aka gano cewa wadannan kati da ya ce sun kone duk anyi amfani da su wajen yin rijistan jarabawa.

Da shi Tanko da Philomena da ta ce maciji ne ya hadiya kudin duk hukumar ta ce za ta hada su ‘Yan sanda.

Share.

game da Author