Wani kwararren likitan kunne da makogoro (ENT) Abdulwahab Anas ya yi kira ga mutane da su guji yawan amfani da na’urar sauraron magana ko kuma sauti a kunnuwar su saboda illar da yin hakan me da shi.
Ya ce yawan haka kan Iya sa kunnen mutum ya toshe, ya zamanto ba ya ji kwata-kwata.
Ya kuma sake yin kira ga mutane su daina yawan tamke kan su da dankwali domin shima yana iya yi wa kunne mutum lahani.
” idan har za a tsaftace kunne za a iya samun kyalle mai tsafta a goge gefe-gefen kunnen amma ba cikin kunnen ba.