TAMBAYA: Wace mata ce cikin matan Annabi ya fi so, kuma me yasa? Tare da Imam Muhammed Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA: Wace mata ce cikin matan Annabi ya fi so, kuma me yasa? Tare da Imam Muhammed Bello Mai-Iyali

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Hakika matan Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa Sallama sunada girman daraja agurin shugaban halitta da mummunai kuma Annabi nason su dukkan su.

Amma Nana Khadija da Nana Aisha suka fi soyuwa ga Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama. Sheikhul Islam Ibnu Taimiyyah yace: fiyayyon matan wannan al-uma sune Nana Khadija da Nana Aisha … Amma wacce tafi wata soyuwa ga Annabi ko tafi wata girman daraja? Lamarine da malamai suka yi sabani acikinsa (Majmu’ul Fatawa 4/ 394).

Dayawan malamai sun karkata akan cewa Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa Sallama yafi son Nana Aishah akan Nana Khadija da sauran matan sa. Hakanan bijiman malamai dayawa suke ganin cewa annabi yafi son Nana Khadija akan Nana Aisha. Kuma dukkan su suna da gamsassun dalilai akan ra’ayoyin su, kuma ingantattu daga Hadisai.

Kadan daga cikin dalilan kowane bangare shi: hadisin da Imamul Bukhari da Muslim suka ruwaito daga Amru Dan Ass, yace na tambayi Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama: Wane mutum kafi so acikin mutane? Sai Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama yace: Aisha…

Sai dai duk da tsananin son da Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama yake wa Nana Aisha, ita Aishan ne ta ruwaito dakan ta kamar yadda hadisin Imamul Bukhari da Musulim suka inganta cewa Aisha ta ce: bana kishi da kowa daga matan Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama, kamar yadda nayi kishi da Khadija, kuma bantaba ganin taba, sai dai Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama yana yawan ambaton ta, kuma sau dayawa Annabi yakan yanka dabba sai ya aikawa kawayen ta da wani bangare, ni kuma nikan ce: kamar dai babu wata mata a duniya sai Khadija, shi kuma sai yace: ta kasance kaza da kaza a gare ni kuma ina da ‘ya’ya da ita.

Wata rana Annabi Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama, yace ma Sayyida Fatima, Aisha fa Masoyiyar baban ki ne, kuma ita ce kadai matata da Wahayi ke sauka a gareni muna cikin bargo daya da ita. Sabo soyayyar Nana Aisha ne Annabi ya zabi yayi jinya a dakin ta, kuma ya rasu a jikin ta sannan aka rufe shi a dakin ta tana makwaftaka da shi. Amma fa
duk da wannan, Annabi ya kasance mai yawan tuna Nana Khadija ne, me yawan Ambaton alkhairin ta, da nema mata gafara.

Akan haka ne, wata rana kishi ya dibi Nana Aisha tace: tsohuwa ce kuma Allah yabaka wadda tafita, a cikin fushi Annabi SAW yace: Sam Wallahi, Allah bai musanyamini ita ba da wadda tafita ba, Khadija ta yi Imani da ni lokacin
da mutane suka kafirce, ta gasgatani lokacin da mutane suka karyatani, ta bani dukiyar ta lokacin da mutane suka hanani, kuma Allah ya azurtani da ‘ya’ya tare da ita banda sauran matan.

Lalle almarine mai matukar wuya wajen ayyana wanda Annabi yafi so tsakanin Nana Khadija da Nana Aisha.

Ibnu Hajar a cikin (Fatahul Bari 7/139) yace: abinda yafi dacewa shi ne aiki da dukkan hadisan, cewa Annabi yana son su, kuma kar a fifita son daya akan ‘yar uwarta. Shi kuwa Ibnu Kasir cewa yayi: a gaskiya dukkan su suna da falala, kuma kowacce nada dalilai da zasu iya fifitata akan ‘yar uwatta. Amma wanda dalilai suka gamsar da shi cewar Annabi SAW yafi son Nana Khadija akan Nana Aisha ko Nana Aisha tafi soyuwa ga Annabi fiye da Nana Khadija, toh zai iya fadin hakan bisa Hujjojin sa na Ilimi. Sai dai dakatawa a cikin wannan mas’alar shi ne tafarki mafi
daidai, sai ace: “Allah shi ne mafi sani”. (Al-Bidayatu Wan-Nihayatu 4/322).

Ya Allah!!! Ka tsare mana Imanin mu da Mutuncin mu. Amin

Imam Muhammad Bello Mai-Iyali

Share.

game da Author