TAMBAYA: Shin su waye ashabul Kahfi, sannan a wani zamani akayi su?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi
Muhammad SAW.
Alkur’ani Mai Girma ya labarto mana tarihin magabata irin su ashabul Kahfi ba don mutanen ba ne, saidai don mu fa’idantu da halin da suka shiga sannan kuma suka tsare imaninsu.
Wannan Qissa ta Ashabul Kahfi Kur’ani ya hakaito ta ne a lokacin da Mushirikan Quraishawa su ke son Jaraba Annabi SAW, sai suka tambayi Yahudawa cewa wacce irin jarabawa za su yima Annabi SAW. Akan hakane Yahudawa suka fadamu cewa su
tambaye shi akan wasu mutane da suka shiga cikin kogo, da wani mutumin da ya zagaye duniya, da Ruhi (RAI).
Suratul Kahfi tana dauke da bayanin Ashabul Kahfi, wato wasu matasa su
bakwai (7) tare da karensu, da suka rayu a zamanin mulkin wani azzalumin sarki Daqayanusa bayan Annabi Isa AS ko kafin zuwansa da sheraka 250. A zamanin ana bautan gumakane karkashin wannan sarki, a garin Amman da ke kasar Jordan a yau.
Sai matasan su 7 suka kyamaci bautan wannin Allah, kuma suka yi imani da Allah sannan suka yi hijira don tsoron tsananin azabar da sarkin zai yi musu idan yakamasu.
Matasan sun gudune don su tsira da Imaninsu, kuma suka shiga wani kogon dutse. Bayan shigarsu sai Allah yasa musu barci tsawon shekaru 300 ko 309 a kirgar watan sama. Sannan Allah ya tashe su daga barcin cikin hikimar sa.
Alkur’ani mai Girma ya ambata wannan kissa kuma a da sauran littafan
kiristanci da na tarihi. Amma akwai sabani da yawa a cikin tarihin wadannan bayin Allah, Kamar haka:
1. Adadin su.
2. Kasar da kogon da suka boye.
3. Shin kafin zuwan Annabi Isa ne ko bayan zuwan sa ne.
4. Sunayen su, da sauran wasu bayanai da yawa. Allahu A’lamu.
Discussion about this post