TAMBAYA: Idan Magriba da Isha’i ya riske mutum a hanya, idan yakai garin sa zai yi magriba ne sannan ya yi isha’i a kasaru?

0

TAMBAYA: Idan Magariba da Isha’i ya riske mutum a hanya, shin idan yakai garin sa zai yi magariba ne sannan yayi isha’i a kasaru?

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi
Muhammad SAW.

Lallai musulmin da Magariba da Isha’i suka riske shi a hanya cikin tafiyar sa, Amma bai tsaya ya sallacesu ba har saida ya dawo anguwarsu ko garinsu, zai yi Magariba raka’a uku sannan ya cika sallar Isha’i raka’a hudu, matukar a kwai sauran lokacin da yakai kimanin minti 3 kafin Huduwar alfijiri.

Akwai hukunci guda hudu (4) game da fita ko dawowa daga tafiya, shin da rana ne? ko da daddare?: Matafiyin ya tashi ne kafin ya sallaci Azahar da La’asar?, ko ya dawo ne kafin ya sallaci Azahar da La’asar?, ko kuma matafiyin ya tashi ne kafin ya sallaci Magariba da Isha’i?, ko
ya dawo ne kafin ya sallaci Magariba da Isha’i. Duk halin da mutum ya samu kansa a ciki, akwai hukuncinsa daga malamai, kamar haka:

1 – MATAFIYIN DA YA TASHI (TAFIYA) KAFIN YA SALLACI AZZAHAR DA LA’ASAR:

a – Idan matafiyi ya tashi tafiyarsa kafin ya sallaci Azzahar da La’asar, kuma a lokacin da zai fara tafiyar ta sa, a kwai kwatankwacin lokacin da za’a iya sallatar Raka’a Uku (3) kafin faduwar Rana (wato, kimanin minti 9 kenan ko fiye da haka), toh zai sallaci Azahar La’asar din sa ne sallar Kasaru. Domin sun same shi a cikin lokacin
tafiya.

b – Amma idan matafiyi ya tashi tafiyar sa kafin ya sallaci Azzahar da La’asar, kuma a lokacin da zai fara tafiyar ta sa, a kwai kwatankwacin lokacin da za’a iya sallatar Raka’a Biyu (2) ne ko kasa da haka kafin faduwar Rana (wato, kimanin minti 6 kenan ko kasa da haka), toh zai sallaci Azzahar sallar gida, domin lokacinta ya wuce a gida, kuma ya
sallaci La’asar din sa sallar tafiya (Kasaru), domin ta same shi a cikin lokacin tafiya.

c – Idan matafiyi ya tashi tafiyar sa kafin ya sallaci Azzahar da La’asar, kuma a lokacin da zai fara tafiyar ta sa, rana ta fadi (wato, lokacinsu ya wuce), toh zai sallaci Azahar da La’asar din sa ne sallar Gida. Domin lokacin su ya wuce kafin tafiyar sa.

2 – MATAFIYIN DA YA TASHI (TAFIYA) KAFIN YA SALLACI MAGARIBA DA ISHA’I:

a – Idan matafiyi ya tashi tafiyarsa kafin ya sallaci Magariba da Isha’i, kuma a lokacin tafiyar ta sa, a kwai kwatankwacin lokacin da za’a iya sallatar Raka’a Uku (3) ko fiye, kafin huduwar alfijiri (wato, kimanin minti 9 kafin Asuba kenan ko fiye da haka), toh zai sallaci Magariba raka’a Uku, domin ita ba’a yi mata kasaru, sannan ya
sallaci Isaha’i Raka’a biyu (Kasaru). Domin ta same shi a cikin lokacin tafiya.

b – Amma idan matafiyi ya tashi tafiyarsa kafin ya sallaci Magariba da
Isha’i, kuma a lokacin da zai fara tafiyar ta sa, a kwai kwatankwacin
lokacin da za’a iya sallatar Raka’a Biyu (2) ko kasa da haka kafin huduwar alfijiri (wato, kimanin minti 6 kenan ko kasa da haka), toh zai yi Magariba Raka’a Uku kuma ya sallaci Isha’i Raka’a hudu (sallar gida), domin lokacinta ya wuce a gida.

3 – MATAFIYIN DA YA DAWO DAGA TAFIYA KAFIN YA SALLACI AZZAHAR DA LA’ASAR:

a – Idan matafiyi ya dawo daga tafiya be sallaci Azzahar da La’asar ba, kuma a lokacin da ya shigo unguwarsu a kwai kwatankwacin lokacin da za’a iya sallatar Raka’a Biyar ko fiye da biyar kafin faduwar rana (wato, kimanin minti 15 kenan ko fiye da haka), toh, zai sallaci Azzahar da La’asar Raka’a hurhudu (Sallar gida).

b – Amma idan ya kasance lokacin da ya shigo unguwarsu a kwai lokaci kwatankwacin da za’a iya sallatar Raka’a hudu ko kasa da hudu kafin faduwar rana (wato, kimanin minti 12 kenan ko kasa da haka), toh, zai sallaci Azzahar Raka’a biyu (Kasaru) amma La’asar zai sallace ta ne Raka’a hudu (Sallar gida).

c – Saidai idan magariba tayi kafin dawowarsa, to zai sallace su ne
Sallar kasaru.

4 – MATAFIYIN DA YA DAWO DAGA TAFIYA KAFIN YA SALLACI MAGARIBA DA ISHA’I:

a – Idan matafiyi ya dawo tafiyarsa kafin ya sallaci Magariba da Isha’i
a cikin lokacin da za’a iya sallatar Raka’a Daya (1) ko fiye da daya kafin huduwar alfijiri (wato, kimanin minti 3 kenan kafin Asuba kenan ko fiye da haka), toh zai sallaci Magariba raka’a Uku, sannan ya sallaci Isaha’i Raka’a Hudu (Sallar gida). Domin ta same shi a cikin lokacin yana gida.

Allah ya yi muku abarka. Amin.

Imam Muhammad Bello Mai-Iyali
Barnawa Low-cost Jumma’at Mosque,
Kaduna.

Share.

game da Author