Shugaban APC ya sha da kyar a hannun ‘yan jagaliya

0

Shugaban APC na Jihar Katsina, Shittu M. Shittu, ya sha da kyar yayin da ‘yan jagaliyar siyasa su ka nemi yi masa rubdugu a Gidan Gwamnatin Jihar Katsina.

Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito cewa wadanda su ka rufe Shittu har jami’an tsaro su ka cece shi da kyar, magoya bayan Bature Masari ne, wanda ya canja sheka daga PDP ya koma APC.

Bature dan’uwa ne ga Gwamna Masari, amma shi ne daraktan kamfen din Nashuni, a karkashin PDP a lokacin zaben gwamna a 2015.

An ce magoya bayan Masari sun fusata sosai da kalaman da Shittu ya yi a lokacin da ya ke karbar su tare da jagoran na su, Bature Masari a jiya Alhamis.

A cikin jawabin da ya yi, Shittu, a matsayin sa na sshugaban jam’iyyar APC, ya nuna shakkun karbar wadanda su ka canja shekar zuwa APC.

“To ni dai ban san Bature Masari sosai ba, na dai sai sun yake mu a lokacin yakin neman zaben gwamna a 2015. Da fatan dai ba ka zo ba ne domin ka yaudare mu, sannan ka gudu ka bar mu.”

Wannan kalami ne ya bata wa magiya bayan Bature Masari rai, har suka yi kumumuwa suka rufar wa Shittu, amma ya ci sa’a jami’an tsaro su ka kwace shi da kyar.

Share.

game da Author