Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, ya bayanna a cikin wani sabon bidiyo, inda ya nuna cewa ya gaji da bala’in da ke bibiyar kungiyar kan yadda su ke yawan rasa dakarun su birjik.
“Na gaji da wannan bala’i; ai har gara ma na mutu, na yi shagada kai tsaye na zarce aljanna.” Haka Shekau ya furka a karshen bidiyon mai mintina goma.
A cikin bidiyon da ya yi magana da Hausa, Shekau bai boye haushin da ya ke ji ba kan yadda sojojin Nijeriya ke yawan karkashe masa dakarun sa.
Da ya ke magana a cikin murya mai kama da wanda ya karaya, Shekau ya roki duk wasu mabiyan sa wadanda ma ke ko ina a cikin kasar nan da ba su dauke da makami, su tashi su fara kisan jama’a bagatatan.
Ya roki su tashi su taya shi yaki har sai an ga karshen kwal uwar daka.
Sai dai kuma ya karyata cewa an kori dakarun sa daga Sambisa. Ya ce za su ci gaba da fafatawa duk kuwa da taron-dangin gangamin sojojin Kamaru da aka yi da na Nijeriya a cikin makon da ya gabata.
WASU KAKKAUSAN KALAMAN DA YA YI:
* Ba mu bukatar ganin kowane dan Najeriya a Kamaru, Chadi, Benin.
* Ina kira ga mabiya na da ke Abuja, Lagos, Benin, Kaduna da ko’ina, duk inda ku ka ga dan Najeriya, ku bindige shi, idan dai abokin gabar mu ne.
* Idan ya jahilci manufar mu, to ku fahimtar da shi.
* Ku kai hari ga duk wani dan Najeriya da ya yi alkawarin kishin kasar sa Najeriya.
* Ku kai hari kan duk wani da ya yi amanna da karatun Boko.
* Ku kai hari kan duk wani da ya riki wata akida ba turbar Annabi (SAW) ba.
* Za mu yaki ‘yan bijilante, da ‘yan Civilian JTF.
* Duk wand aba zai iya zuwa ya taya mu yaki a nan ba, to ya taya mu daga duk inda ya ke.
Discussion about this post