Shehu Sani ya ziyarci ofishin Jamb da masu kama maciji

0

Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya ziyarci ofishin shirya jarabawa na shiga Jami’o’i ‘JAMB’ tare da ‘Gardawa’ masu kama maciji.

Idan ba a manta ba wani ma’aikacin hukumar Jamb ya fadi cewa maciji ya hadiye miliyan 36 a asusun hukumar.

” Ina jin haka ne naga ya dace in bada na wa gudunmuwar, inda na je na dauko masu kama maciji a daga mazabata domin su zo su taimaka wajen kamo wannan maciji, da wasu idan akwai a dazukan da ke gefen hukumar.

” Idan har maciji zai iya hadiye miliyan 36, to wata rana zamu waye gari a kasar nan macizai sun hadiye asusun ajiyan kudin mu dake kasar waje ko kuma kudaden da muka tara daga asusun TSA.” Inji Shehu Sani

Bayan haka daya daga cikin masu kama macijin, Tasiu Abdurrasheed, ya bayyana cewa sana’ar kama maciji, gadar ta yayi shekaru 20 da suka wuce, kuma bai taba ganin macijin da ya hadiye maciji ba.

A karshe Kakakin hukumar Fabian Benjamin ya nuna takaicin sa ga abinda ya faru, cewa hakan abin ayi juyayi ne akai, ba ya zama abin raha ba.

Share.

game da Author