Jami’in kungiyar Kiwon Lafiya ta Duniya WHO Terna Nomhwange ya bayyana cewa za su yi wa mutane miliyan 1.2 alluran rigakafin cutar shawara a jihar Barno.
Nomhwange wanda ya sanar da haka wa manema labarai a sansanin ‘yan gudun hijira dake Bakkassi a Maiduguri ya ce sun ware miliyan daya na alluran rigakafin cutar domin yi wa yara ‘yan watanni tara zuwa manya ‘yan shekaru 45 a kananan hukumomi 25 a jihar.
” idan mun kammala da sansannin Bakkassi za kuma mu tafi sansanin Gwoza sannan da sauran wuraren da suke fama da cutar a jihar.”
Ya kuma kara da cewa kungiyar su ta hada hannu da gwamnati don dakile yaduwr cutar a jihohi 16 da ya hada da Abia, Anambra, Enugu, Kano, Katsina, Kogi, Kwara, Kebbi, Legas, Nasarawa, Neja, Oyo, Filato, Zamfara da sauransu.