Sarki Sanusi ya dakatar da masu unguwanni biyu a Kano

0

Mai martaba sarkin Kano Muhammad Sanusi II ya dakatar da dakacin unguwan Jibga, Shu’aibu Magaji da ke karamar hukumar Makoda a jihar.

Sarki Sanusi ya dakatar da Magaji ne saboda laifin hana a yi wa yaran unguwar sa allurar rigakafi.

Masarautar ta kuma zarge sa ta karban jinginan wani kabari don bashin da ya ba wani mutum cewa hakan ya karya dokar masu unguwanin jihar.

Bayan haka kuma Sarki ya dakatar da mai unguwan Badawa, Ibrahim Badawa dake karamar hukumar Nasarawa saboda goyan bayan ta’adancin da dansa ke yi a unguwa.

Masarautar Kano ta ce za ta dawo da su ne bayan kwamitin da ta kafa ta kammala bincike kan laifukan da suka aikata.

Share.

game da Author